EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati

EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun yi caraf da wakilin al’ummar Akwa Ibm ta Arewa maso gabas a majalisar dattawa, Sanata Bassey Akpan kan badakalar kudi naira miliyan dari uku da dubu dari uku, N303m.

Jaridar The Punch ta ruwaito EFCC ta cafke Sanatan ne da laifin amsan wasu motoci da darajarsu ta kai naira miliyan 303 daga hannu wani babban hadimin tsohuwar ministan mai, Diezani Allison Madueke, Babajide Omokore, wanda a yanzu haka yake fuskantar tuhume tuhumen satar kudin al’umma.

KU KARANTA: Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo

Wani rahoto daga hukumar EFCC wanda majiyar Legit.ng ta gano ya bayyana cewa a zamanin da Sanatan yake kwamishina a gwamnatin tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Sanata Godswill Akpabio, ya baiwa Omokore kwangiloli, don haka ake ganin motocin a matsayin cin hanci ya karba.

EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati

Akpan

Haka zalika, Kaakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya tabbatar da kama Sanatan, inda ya bayyana ma majiyarmu a cikin wani sakon karta kwana da ya aika mata yana cewa: “Eh, a ranar Talata muka kama shi”

“Sanata Bassey ya karbi wata mota kirar BMW X5 BP da kudinta ya kai naira miliyan 50, wata motar kirar Infinity QX56BP da kudinta ya kai naira miliyan 45, Range Rover da kudinta ya kai naira miliyan 40, Toyota Hiace guda biyar da kudinsa ya kai naira miliyan 43, Hilux guda shidda da kudinsu ya kai naira miliyan 42 da wasu motoci da jimillan kudinsu ya kai naira miliyan 83, dukkaninsu daga wajen Omokore, wanda ya bashi kwangilar aikace aikace a jihar.” Inji rahoton.

Rahoton ya kara da cewa hukumar ta gayacce shi a baya, bas au daya ba, ba sau biyu ba, amma yayi kunnen kashi, wannan dalilin ne ya sanya jami’an hukumar damko wuyarsa. Sai dai Sanatan ya musanta karbar kayan a matsayin cin hanci, inda yace Omokore abokinsa ne.

“Kyautar motocin Omokore ya bani don tsaron lafiyata, abokina ne, mun san juna sama da shekaru 19 da suka gabata, haka zalika ya bani su ne a matsayin gudunmuwarsa ga takarar gwamnan jihar Akwa Ibom da na tsaya a shekarar 2014.” In ji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel