Siyasar Kano: Yan majalisar dokokin jihar Kano sun mayar da wukakensu cikin kube

Siyasar Kano: Yan majalisar dokokin jihar Kano sun mayar da wukakensu cikin kube

Yan majalisun dokokin jihar Kano su ashirin da hudu, 24 da suka dauki gabaran tsige Kaakakin majalisar dokokin jihar Kano sun mayar da wukakensu cikin kube sakamakon shiga tsakani da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito mai magana da yawun yan majalisa, tsohon Kaakakin majalisar, Kabiru Rurum ya bayyana matsayinsu, a yayin dayake ganawa da manema labaru a daren Laraba 16 ga watan Mayu a garin Kano.

KU KARANTA: Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo

“Muna tabbatar muku da cewa gwamnann jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da shuwagabancin jam’iyyarmu sun sa baki a bahallatsar da ta dabaibaye majalisar dokokin jihar Kano, don ganin an samu sulhu, kuma mun gamsu da matakin da suka dauka.” Inji shi.

Siyasar Kano: Yan majalisar dokokin jihar Kano sun mayar da wukakensu cikin kube

Majalisar dokokin jihar Kano

Sai dai ya bayyana sharuddan da suka gindaya ma Kaakakin majalisar, wadanda kuma yace gwmanan jihar Kano dukkanin wadanda ke da hannu cikin bahallatsar sun aminta da su, sune kamar haka:

1- Yusuf Abdullahi ya cigaba da zama Kaakakin majalisa

2- Kabiru Rurum ya dare kujerar mataimakin sabon Kaakakin majalisa

3- Mohammed Bello Butu-butu ya zama sabon shugaban masu rinjaye

4- Bappa Babba Dan Agundi ya zama sabon mai tsawatarwa

5- Sanusi Usman Bataiya ya zama sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

6- Ayuba Labaran Durum ya zama sabon bulaliyar masu rinjaye

Daga karshe ya bukaci jama’a dasu kwantar da hankulansu, cewa zaman lafiya ya dawo, kuma zasu cigaba da yi ma doka da ka’ida biyayya, sa’annan yace majalisar zata koma zamanta a ranar Alhams, 17 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

https://www.youtube.com/watch?v=4nD0mwh8Yp4

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel