Dole a sa kudin tallafin man fetur cikin kasafin kudin bana – Bukola Saraki

Dole a sa kudin tallafin man fetur cikin kasafin kudin bana – Bukola Saraki

- Bukola Saraki ya nemi a sa kudin tallafin man fetur cikin kasafin bana

- Shugaban Majalisar ya nemi Shugaban kasa ya sakala kudin daga baya

- A makon nan ne ‘Yan Majalisun Najeriya su ka amince da kasafin kudin

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya nuna cewa har yanzu ba a kammala aiki kan kasafin kudin wannan shekarar ba duk da cewa Majalisar ta amince da shi a jiya.

Dole a sa kudin tallafin man fetur cikin kasafin kudin bana – Bukola Saraki

An nemi Shugaba Buhari ya sa kudin tallafin fetur cikin kasafi

Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya yabawa kokarin da ‘Yan Majalisar kasar su kayi na aikin kasafin kudin na bana sai dai yace akwai wata babbar matsala guda. Bukola Saraki yace ba a sa kudin tallafin fetur cikin kasafin ba.

Bukola Saraki yace za su yi kokarin ganin sun yi abin da ya dace game da kudin da Najeriya ke kashewa wajen biyan tallafin man fetur. Saraki yace ya kamata asa wannan kudi cikin kasafin kudin bana domin ayi ke-ke-da-ke-ke.

KU KARANTA: Gwamnati za ta bada aikin Kano zuwa Garin Bauchi

Kudin da Najeriya ke kashewa domin biyan ‘Yan kasuwa tallafin man fetur ya doshi Naira Tiriliyan guda don haka ne Shugaban Majalisar yake ganin ya dace a sa kudin cikin kasafin bana domin a san yadda aka kashe dukiyar kasar.

Idan har aka kara kudin tallafin man fetur din dai Najeriya na iya kashe Naira Tiriliyan 10 a shekarar 2018. Yanzu dai an amince da kasafin kudin Tiriliyan 9.1 a shekarar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel