Majalisa ta kara Biliyan 500 cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya aika masu

Majalisa ta kara Biliyan 500 cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya aika masu

Bayan sama da watanni 6 ne dai Majalisar Najeriya ta iya amincewa da kundin kasafin kudin wannan shekarar. Idan ba a manta ba tun a Watan Nuwamban bara aka mikawa Majalisa kasafin na bana.

Majalisa ta kara Biliyan 500 cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya aika masu

‘Yan Majalisa sun karawa kan su Biliyan 14 a kasafin kudin bana

Sai dai jiya ne Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilan Kasar su ka yi na’am da kundin kasafin na bana inda aka kara har Naira Biliyan 500 a cikin kasafin. Yanzu dai Najeriya na iya kashe sama da Tiriliyan 9 a bana.

A bara dai Shugaba Muhammad Buhari ya gabatar da kasafin Tiriliyan 8.6 ne a gaban Majalisar. Shugaban Kwamitin na kasafin kudi a Majalisar Dattawa Danjuma Goje yace Fadar Shugaban kasa ta san da wannan kari.

KU KARANTA: Za a kashe Biliyoyin kudi domin yashe Kogin Kwara

An kara kasafin na bana ne saboda karin da aka samu na farashin gangar man Najeriya a kasuwar Duniya. Da farko an yi lissafin gangar mai a kan N45 amma kuma yanzu man ya kara kudi. Yanzu an sa kudin man ne a kan N51.

Rarar da aka samu dai wajen cinikin man za su tafi wajen yin ayyuka ne na gina kasan da ba a sa su cikin kasafin kudin ba. Ita ma dai Majalisar ta kara kudin ta daga Naira Biliyan 125 zuwa Naira Biliyan 139 a kasafin kudin bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel