Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Sojojin hadin gwiwa na kasar Kamaru da Najeriya sun yi nasarar hallaka mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram dai dai har guda goma sha biyar, 15 a wasu arangama daban daban da suka yi a kudancin tafkin Chadi.

Legit.ng ta ruwaito mataimakin daraktan watsa labaru na Operation lafiya dole kanal Onyeama Nwachuku ne ya bayyana haka a ranar Laraba 16 ga watan Mayu, inda yace Sojojin sun yi ma yan ta’addan dirar mkiya ne a kauyukan dake makwabtaka da tafkin Chadi.

KU KARANTA: Uwargidar shugaban kasa ta karbi bakoncin shuwagabannin jam’iyar matan Arewa

Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Barnar

A wannan arangama ne Sojojin suka fatattaki yan ta’addan daaga mafakarsu, inda tare da kashe guda 11, inda wasu Sojojin suka yi ma sauran da suka tsere tara tara, a kauyukan Firgi da Moula, suka yi musu kwantar bauna, inda suka hallakasu.

A sakamakn samamen da Sojoji suka kai, sun samu nasarar ceto Maza 4, mata 33 da kananan yara 16, a jimlace Sojojin sun ceto rayukan mutane 53, haka zalika sun kwato makamai da suka hada da babura 4, A daidaita sahu 2, bindigu, injinan ban ruwa 6, Janareta 2, tutocin Boko Haram 2, kayan Sojoji, kyamara, magunguna da kayan kanikanci.

Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Harin

A wani labarin kuma, wani dan kunar bakin wake ya tashi kansa da daurin bam da yayi jigida dasu a jihar Maiduguri, inda ya hallak Sojoji sa kai su biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel