Da duminsa: Shugaba Buhari na wata ganawar sirri da jiga-jigan jam'iyyar APC a Aso Villa

Da duminsa: Shugaba Buhari na wata ganawar sirri da jiga-jigan jam'iyyar APC a Aso Villa

Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya wata liyafar cin abinci na musamman ga shugabanin jam'iyyar APC na Kudu maso yamma a fadar Aso Villa da ke Abuja.

An fara taron ne misalin karfe 8.35 na daren yau a dakin taro na Banquet lokacin da shugaba Buhari ya iso dakin taron.

Wanda suka samu hallartan taron sun hada da shugaban jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu da Cif Bisi Akande da kuma Ciyaman na jam'iyyar APC, John Odigie-Oyegun.

Da duminsa: Shugaba Buhari na wata ganawar sirri da jiga-jigan jam'iyyar APC a Aso Vila

Da duminsa: Shugaba Buhari na wata ganawar sirri da jiga-jigan jam'iyyar APC a Aso Vila

Sauran sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da Segun Oni ministan karafa da kuma dan takaran gwamnan jihar Ekiti a zabe mai zuwa, Kayode Fayemi.

KU KARANTA: Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi

Gwamnonin da suka samu hallarta sun hada da Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Abiola Ajimobi na jihar Oyo da gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura.

Wasu 'yan majalisar tarayya da ministoci na yankin na kudu maso yamma sun sami hallarar taron.

Kafin a sanya a labule a taron, an sanar da cewa Fayemi da Tinubu za suyi takaitun jawabi a yayinda Odigie-Oyegun da shugaba Buhari za su gana bayan walimar.

Ana nan ana gudanar da taron a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel