Jami'an kwastam sun kama motocin alfarma 30 a jahohi 2 na Najeriya

Jami'an kwastam sun kama motocin alfarma 30 a jahohi 2 na Najeriya

Jami'an rundunar hukumar hana fasa kwauri ta tarayyar Najeriya dake a shiyyar dake kula da yanki na A karkashin shugabancin Mohammed Uba a ranar Laraba ta sanar da samun nasarar cafke motocin alfarma akalla 30 da kudin su ya kai darajar Naira biliyan 1.

Kamar dai yadda rundunar ta bayyana, an kama motocin ne lokacin da ake kokarin shigowa da su ta kan iyakar Najeriya da kasashen jamhuriyar Kamaru da Benin a jahohin Legas da Ogun dukkan su a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan.

Jami'an kwastam sun kama motocin alfarma 30 a jahohi 2 na Najeriya

Jami'an kwastam sun kama motocin alfarma 30 a jahohi 2 na Najeriya

KU KARANTA: Sarkin musulmi ya ce an ga watan Ramadana

Legit.ng ta samu cewa Mista Uba Mohammed ya kuma kara da cewa tuni dai rundunar ta mallaka motocin ga gwamnatin tarayya kamar yadda doka ta tanada.

A wani labarin kuma, Wata mata mai shekaru 39 a duniya kuma mai suna Esther Olawole dake a jihar Osun ta shiyyar kudu maso yammacin kasar ta gurfana a gaban kuliya bisa zargin da ake yi mata na burmawa wani babban malamin addinin kirista fasassar kwalba.

Dan sanda mai gabatar da kara dai mai suna Isifekta Emmanuel Abdullahi tun farko ya shaidawa kotun cewa wadda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Mayu shekarar 2018 da misalin karfe 6 na yamma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel