Buhari ya bayyana matsayar sa game da kafa kasar Falasdinawa

Buhari ya bayyana matsayar sa game da kafa kasar Falasdinawa

Ma'aikatar harkokin waje ta tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sake jaddada matsayin ta akan yadda za'a iya kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa na kasar Isra'ila da yankin Falasdinawa.

Kamar dai yadda ofishin jakadancin kasar Najeriya din dake a kasar Isra'ila ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar ta manema labarai, ya ce har yanzu Najeriya na akan bakan ta na baiwa yankin na Falasdinawa yancin cin gashin kan su.

Buhari ya bayyana matsayar sa game da kafa kasar Falasdinawa

Buhari ya bayyana matsayar sa game da kafa kasar Falasdinawa

KU KARANTA: Shehu Sani na fuskantar matsin lamba ya koma PDP

Legit.ng ta samu dai cewa yankunan biyu na fama da rikici ne shekaru da dama da suka gabata musamman ma bisa ikon mallakar kasar yankin da kuma wuraren addinai masu tarihi.

A wani labarin kuma, Labarin da ke iso mana daga majiyoyi da dama na nuni ne da cewa jama'a a jahohi da dama na Najeriya sun ga watan Ramada a farkon daren yau Laraba, 16 ga watan Mayu, shekarar 2018.

Wannan dai ta tabbata ne a cikin wata sanarwa daga bakin Sarkin musulmi inda ya tabbatar da ganin watan a jihohi da dama kuma hakan a bisa al'ada na nufin watan na Ramadana ya tsaya kenan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel