Dalilin da yasa kotu ta bayar da belin Dino Melaye

Dalilin da yasa kotu ta bayar da belin Dino Melaye

- Kotun jihar Kogi wacce ke zama a Lokoja a ranar Laraba ta bayar da Sanata Dino Melaye, wanda ake tuhuma da laifin ta’addanci da kuma amfani da makami tare da wasu mutane biyu akan beli

- Justis Nasir Ajanah ya bayar dashi belin, bayan lauyan dake wakiltarsa a kotun, Mike Ozekhome (SAN), ya rubutawa kotun bukatarsa ta karbar wanda yake wakiltar akan beli

- Kotun ta bayar da Sanata Dino Melaye, akan belin N10m da kuma wanda zai tsaya masa ya kuma biya masa kudaden

Kotun jihar Kogi wacce ke zama a Lokoja a ranar Laraba ta bayar da Sanata Dino Melaye, wanda ake tuhuma da laifin ta’addanci da kuma amfani da makami tare da wasu mutane biyu akan beli.

Justis Nasir Ajanah ya bayar dashi belin, bayan lauyan dake wakiltarsa a kotun, Mike Ozekhome (SAN), ya rubutawa kotun bukatarsa ta karbar wanda yake wakiltar akan beli.

Dalilin da yasa kotu ta bayar da belin Dino Melaye

Dalilin da yasa kotu ta bayar da belin Dino Melaye

Ajanah ya bayyana cewa hujojjin da aka gabatar ya nuna cewa Melaye na fama da wasu cututuka, don haka kotu ta yanke shawarar bayar da belinsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah yayi majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2018

Kotun ta bayar da Sanata Dino Melaye, akan belin N10m da kuma wanda zai tsaya masa ya kuma biya masa kudaden, sannan kuma ya kasance mai halin biyan kudin ne tare da bayar da adireshi wanda ake da tabbashin samunsa a ta nan.

Mike Ozekhome, wanda ke wakiltar wanda ake tuhumar, yace wannan hukunci da kotun tayi ya kara daga martabarta a cikin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel