Za a yi kacibus tsakanin Saraki da Sifeton ‘yan sanda a taron da Buhari ya kira a daren yau

Za a yi kacibus tsakanin Saraki da Sifeton ‘yan sanda a taron da Buhari ya kira a daren yau

A daren yau ne za yi wata ganawa tsakanin Buhari da shugaban majalisar Dattijai, Abubakar Bukola Saraki, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Majalisar Dattijai ta fitar da sunayen mambobinta 10 da zasu raka Saraki taron na daren yau.

Mambobin 10 da zasu raka Saraki sune; Shugaban masu rinjaye na majalisar, Ahmed Lawan, Bulaliyar majalisa, Olusola Adeyeye, shugaban marasa rinjaye, Godswill Akpabio, Sanata Oluremi Tinubu, da Sanata Raji Rasaki.

Ragowar sune Sanata Aliyu Wammako, Sanata Sam Egwu, Sanata Danjuma Goje da Sanata Abdullahi Adamu.

Za a yi kacibus tsakanin Saraki da Sifeton ‘yan sanda a taron da Buhari ya kira a daren yau

Saraki da Sifeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris

Saraki zai gana da Buhari ne a kan batun cewar shugaban ‘yan sanda na shirin sahafa masa jar lamba domin samun dammar makala masa laifin da zai bashi dammar bincikar sa.

DUBA WANNAN: Ta azabtar da yaro bisa zargin maita, 'yan sanda sun yi caraf da ita

Sau biyu majalisar Dattijai na gayyatar Sifeto Idris ya bayyana a gaban ta amma hakan bata samu ba. Saraki, cikin fushin rashin bayyana Sifeto Idris, ya kira shi da makiyin siyasa. Kalamin da basu yiwa hukumar ta ‘yan sanda dadi ba, domin har fitowa tayi ta mayar da raddi ga Saraki.

Majalisar dattijai na son Sifeto Idris ya bayyana gabanta ne domin yi masa titsiye a kan badakalar da ta kai jami’an hukumar ‘yan sanda kama Sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel