Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

- Ana ta tafkwa mahawara mai zafi tsakanin magoya bayan shugaba Buhari da Atiku Abubakar

- Mahawarar ta samo asali ne bayan Atikun ya furta cewa idan ya lashe zaben 2019 zai sayar da matatun man fetur da 'yan kasuwa

- Su kuma magoya bayan Buhari sun ce idan gwamnati ta zame hannu ta daga fannin man fetur din, farashin abubuwa za su hauwhawa kuma talaka zai wahala

Mahawara mai zafi ta barke tsakanin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar saboda kiraye-kirayen da Atiku ya yi na cewa ya kamata gwamnati ta zame hannun ta ciki wasu bangarorin fanin man fetur da iskar gas na Najeriya.

Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

A yayin da magoya bayan shugaba Buhari a karkashin kungiyar Buhari Media Organisation ke cewa bukatar Atikun na cewa gwamnati ta sakar wa 'yan kasuwa wasu bangarorin man fetur musamman gina matatun mai ganganci ne da ba zai haifar wa al'umma alheri ba, Magoya bayan Atiku sun ce rashin wayewa da ilimin tattalin arziki na zamani yasa gwamnatin Buharin ta ki amincewa da hakan.

KU KARANTA: Naci dambun kuturu: Saraki ya kara gayyatar Sifeto Idris a karo na uku domin amsa wasu tambayoyi

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ake sa ran zai yi takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP ya ce idan har ya yi nasarar zama shugaban kasa bayan zaben 2019, mayar da fanin man fetur da iskar gas hannun yan kasuwa yana daya daga cikin abubuwan da zai aiwatar.

Kungiyar magoya bayan Buhari ta ce abin mamaki ne yadda mutum kamar Atiku zai rika kirar cewa a sayar da matatun man Najeriya duk da cewa ya san hakan zai sanya farashin man fetur din ya yi tashin gwauron zabi wanda hakan zai kawo hauhawar farashin kayayaki a kasuwani.

"Shawarar mu shine duk wanda ya ke bukatar kina matatan man fetur ko iskar gas ya tafi a samo lasisi daga hukuma don ya kafa nasa. 'Yan kasuwa kamar Alhaji Aliko Dangote ya yi hakan kuma ya gina matatan mai a Legas wanda ke samar da gangan man fetur 650,000 a kowane rana," inji kungiyar magoya bayan Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel