Hameed Ali ya yiwa ma'aikatan Kastam gargadi akan neman Kudi a madadin jajircewa bisa aiki

Hameed Ali ya yiwa ma'aikatan Kastam gargadi akan neman Kudi a madadin jajircewa bisa aiki

Kanal Hamid Ali, Kwanturola janar na hukumar kastam ya gargadi dukkanin ma'aikatan sa akan kauracewa neman a musanya masu wuraren aiki da manufar samun abin hannun na kudi a madadin tsayawa jajirce bisa aiki.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a yayin bikin karin matsayi ga wasu ma'aikatan hukumar da suka hadar da na jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Jigawa, Kebbi da kuma Zamfara da aka gudanar a jihar ta Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban hukumar Mista Uda-Aka Emmanuel, shine ya wakilci Kanal Hamid yayin wannan biki na karin matsayi ga ma'aikata 1, 977 fadin kasar nan.

Hameed Ali ya yiwa ma'aikatan Kastam gargadi akan neman Kudi a madadin jajircewa bisa aiki

Hameed Ali ya yiwa ma'aikatan Kastam gargadi akan neman Kudi a madadin jajircewa bisa aiki

Kanal Ali ya gargadi ma'aikatan akan jajircewa wajen sauke nauye-nauyen aiki na yiwa kasar su hidima da ya rataya a wuyan su.

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa ya tsarkake Kashe-Kashen jihar Benuwe daga duk wani Tuggu

Shugaban hukumar ya kuma tunatar da ma'aikatan akan cewa karin matsayin yana tafiya ne tare da karin nauyi, inda ya nuna damuwar sa dangane da yadda mafi akasarin ma'aikata na wannan zamani suke rike mukamai ba tare da sanin nauyin da ya rataya a wuyansu.

Daga karshe Kanal Ali ya shawarci ma'aikatan akan su kasance masu tarayya da hakuri da juriya a kowane lokaci na gudanar da aikin su da zai taimaka kwarai da aniyya wajen kawo ci gaba ga hukumar da kuma kasar Najeriya baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel