Da amincewar Fadar Shugaban Kasa muka yiwa Kasafin Kudin 2018 Kwaskwarima - Shehu Sani

Da amincewar Fadar Shugaban Kasa muka yiwa Kasafin Kudin 2018 Kwaskwarima - Shehu Sani

A ranar Larabar da ta gabata ne Honarabul Shehu Sani, Sanata mai wakiltar Jihar Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa, majalisar dokoki ta tarayya ta samu yin karin adadi cikin kasafin kudin 2018 daga N8.612trn zuwa N9.120trn da amincewa ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Sanata Shehu ya yi wannan fashin baki ne na bayar da tabbaci a shafin sa na sada zumunta na twitter.

Sanatan ya bayyana cewa, majalisar ba tayi gaban kanta ba wajen sauyi na adadin kasafin kudin 2018 face sai da tuntuben fadar shugaban kasa.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Sanata Danjuma Goje, jagoran kwamitin kasafin kudin ya gabatar da sakamakon bincike akan sabon kasafin kudin a farfajiyar majalisar dattawa.

KARANTA KUMA: Mabarata sun yi watsi da goma ta arziki, sun koma bakin aiki a garin Abuja

Ana sa ran shigar da kasafin kudin cikin dokar kasa kamar yadda majalisar wakilai ta bayyana a jiya Talata.

Legit.ng ta fahimci cewa, kawowa yanzu watanni shidda kenan tun da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisar inda ya nemi amincewar ta wajen shigar da shi cikin dokar Kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel