Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Jagoran shirya zaben sharan fage na gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, wanda za’ayi a jihar Ekiti cikin watan Yuli, Tanko Almakura ya gabatar da ministan ma’adinai, Dr. Kayode Fayemi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ya gabatar da shi ga shugaban kasar a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu a matsayin dan takarar jam’iyyar a fadar shugaban kasa, Abuja.

Amma ministan wanda bai rigada ya mika takardan ajiye aikinsa ga shugaban kasar ba tukuna yace har yanzu kundin tsarin mulkin 1999 ta bashi kariyan cigaba da kasancewa kan mukaminsa na tsawon kwanaki 30 kafin zabe.

Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Ya bayyana cewa Ekiti na neman agaji ta ko ina don kawo karshen rashin albashi da talauci da al’umman kasar ke cigaba da fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Matar shekarau ta tallafawa mabukata da kuma zawarawa

Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Yanzu Yanzu: Almakura ya gabatar da Fayemi ga Buhari

Yayi alkawarin dawo da kasar kan tafarki na gari tare da kawo cigaba da nasarori a gwamnatin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kayode Fayemi ya sanar da cewa zai ajiye aikinsa na minista nan da mako guda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel