Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda na shirin kulla min sharri - Bukola Saraki

Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda na shirin kulla min sharri - Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa ana wasu shirye-shiryen kulla masa sharri kuma sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Kpotum Idris, ne ke jagorantan shirin.

Saraki ya ce an damke wasu yan daba a jihar Kwara kuma sifeto janar ya bada umurnin cewa a kawo su Abuja saboda suyi maganganu da ka iya daure shugaban majalisan.

Saraki yace mutane masu karfin mulki su daina amfani da kujeransu wajen musgunawa abokan hamayya.

Sanatocin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan al’amarin dauki daya-daya da hukumar yan sanda ke musu. Daga cikin sanatocin da su kayi Magana shine sanata Kabiru Marafa na jihar Zamfara, sanata Isa Hamman Misau na jihar Bauchi da kuma sanata Abdullahi Adamu.

KU KARANTA: ‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma - Inji ‘Yan Shi’a

Wannan abu na faruwa ne yayinda hukumar ke cigaba da garkame sanata Dino Melaye wanda ake zargi da daukan nauyin wasu masu garkuwa da mutane ta hanyar basu kudi da makamai.

A yau dai kotu ya basa belin N10million amma gwamnatin tarayya ta bukaci kotu ta janye wannan beli da aka bashi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel