Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye kan wasu makuden miliyoyi

Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye kan wasu makuden miliyoyi

A yau Laraba ne wata kotu da ke jihar Kogi ta bayar da belin Sanata Dino Melaye mai wakiltar yankin kogi ta yamma.

Kotun ta bayar da belinsa ne a kan kudi N10 miliyan kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Alkalin kotun, Nairu Ajanah ya ce kotun ta bayar da belin ne saboda rashin lafiya da sanatan ke fama dashi.

Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino melaye kan wasu makuden miliyoyi

Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino melaye kan wasu makuden miliyoyi

Hukumar 'Yansandan Najeriya ne ta gurfanar da sanatan a gaban kuliya bisa zarginsa da safarar bindigogi wanda aka ce ya rabawa wasu matasa da 'yan baranda.

A cewar hukumar 'Yan sanda biyu daga cikin 'yan barandan da aka kama sun amsa cewa Sanata Melaye ne ya siya musu bindigogi kuma shi ke daukan nauyin su.

KU KARANTA: Kasar Amurka ta aike da sakon Azumi ga musulmin duniya

A makonnin baya ne dai Sanata Dino Melaye ya daka tsalle daga cikin motar 'yan sanda a yayin da ake hanyar tafiya dashi kotu inda ya ce wai ana son a tafi dashi jihar Kogi ne don a kashe shi.

Hakan yasa Sanatan ya sami raunuka kuma a halin yanzu yana wata asibiti a Abuja inda ya ke karban magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel