Tun yanzu? Rikici ya barke a sabuwar jam’iyyar Obasanjo, ADC

Tun yanzu? Rikici ya barke a sabuwar jam’iyyar Obasanjo, ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Ekiti ya shiga babban rikici yayinda dan takaranta, Ayodele Adesua, ya lashi takobin cewa ba zai ajiye niyyarsa na takara ga kowani ma’aluki ba sakamakon wani munafurci da wani shugaban jam’iyyar ke yi.

Za ku tuna cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya mara goyon bayansa ga jam’iyyar ADC kuma yayi kira ga kungiyoyin hamayya da wasu masu ruwa da tsaki suyi amfani da jam’iyyar wajen kada shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Ayodele Adesua ya ce tsohon shugaban hukumar NIMC da ya fice daga jam’iyyar APC kuma yayi murabus daga kujeran, Olagunsoye Oyinlola, na shirin cin mutunsa akan zaben jihar Ekiti da za’ayi a watan Yuli.

Tun yanzu? Rikici ya barke a sabuwar jam’iyyar Obasanjo, ADC

Tun yanzu? Rikici ya barke a sabuwar jam’iyyar Obasanjo, ADC

Mr Adesua ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranan Lahadin da ya gabata a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

KU KARANTA: Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kada ya saurarawa Barayi

A wani jawabi da ya saki jiya Talata, Adesua ya ce Mista Olagunsoye Oyinlola da kokarin maye gurbinsa da abokinsa, Dare Bejide, domin takara karkashin leman jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel