Buhari bai koyi darasi daga abubuwan da ya fuskanka a baya ba - Balarabe

Buhari bai koyi darasi daga abubuwan da ya fuskanka a baya ba - Balarabe

- Manyan Dattawa jarewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa, da kuma tsohon dan majalisar dokoki, Dr. Junaid mohammed, sun kalubalanci shugaba Buhari, inda sukace wannan gwamnatin ba abunda tayi game da rashawa kamar na lokacin 1983 zuwa 1985

- Balarabe yace duk da cewa yaki da rashawa yasa aka sauke shugaba Buhari a wancan lokacin amma ya akayi yake bari rashawa na kokarin yakarsa a wannan lokacin a gwamnatinsa, baya daukar matakan da suka kamata don magance matsalar

- Dr. Junaid Mohammed a nasa bangaren yace shugaba Buhari karya yake yiwa mutane yace saboda rashawa ne kadai aka cire shi daga gwamnati, akwai abubuwa da dama a lokacin, 1985 wadanda har yanzu baya so ya amince dasu kuma matsala ne

Manyan Dattawa arewa biyu, tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa, da kuma tsohon dan majalisar dokoki, Dr. Junaid mohammed, sun kalubalanci shugaba Buhari, inda sukace wannan gwamnatin ba abunda tayi game da rashawa kamar na lokacin 1983 zuwa 1985.

Balarabe yace “duk da cewa yaki da rashawa yasa aka sauke shugaba Buhari a wancan lokacin amma ya akayi yake bari rashawa na kokarin yakarsa a wannan lokacin a gwamnatinsa, baya daukar matakan da suka kamata don magance matsalar.”

Buhari bai koyi darasi daga abubuwan da ya fuskanka a baya ba - Balarabe

Buhari bai koyi darasi daga abubuwan da ya fuskanka a baya ba - Balarabe

Dr. Junaid Mohammed a nasa bangaren yace “shugaba Buhari karya yake yiwa mutane yace saboda rashawa ne kadai aka cire shi daga gwamnati, akwai abubuwa da dama a lokacin, 1985 wadanda har yanzu baya so ya amince dasu kuma matsala ne har yau.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta rubutawa kasar Ingila da Amurka wasika akan shiga takardun kula da lafiyar shugaba Buhari da ake zargin anyi ba tare da izini ba

Shugaba Buhari a wurin taron bude sabuwar helikwatar Ofishin yaki da rashawa da cin hanci ta kasar nan a wadda aka gina a birnin tarayya, a ranar Talata yace lokacin mulkinsa na zamanin Soja an cireshi daga kan mulki ne domin yana fada da rashawa da cin hanci, inda har aka tsareski a gidan yari na tsawon shekaru uku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel