Wani dan sanda ya harbe kan sa a kan canjin wurin aiki

Wani dan sanda ya harbe kan sa a kan canjin wurin aiki

- Wani dan sanda a kasar Kenya ya saka bindigar sa a baki sannan ya sakarwa kan sa harsashi saboda an dauke shi daga wurin aikin sa

- Abokan dan sandan sun bayyana cewar yana cikin halin matsananciyar damuwa bayan yin aiki na tsawon shekaru uku a wuri guda

- Wani jami’in ‘yan sanda a yankin gabashin Kenya, Mohamud Saleh, ya bayyana cewar sun fara binciken mutuwar dan sandan

Wani dan sanda a kasar Kenya ya saka bindigar sa a baki sannan ya sakarwa kan sa harsashi saboda an dauke shi daga wurin aikin sa a garin Garissa ya zuwa wurin da bai kai inda yake ba, bayana ya shafe fiye da shekaru ukun yana aiki a wurin.

Wani dan sanda ya harbe kan sa a kan canjin wurin aiki

'Yan sandan kasar Kenya

Kamfanin dillancin labarai na Standard Reports ya rawaito cewar, abokan dan sandan sun bayyana cewar yana cikin halin matsananciyar damuwa bayan yin aiki na tsawon shekaru uku a wuri guda amma maimakon a yi masa canji mai kyau sai aka tura shi ofishin ‘yan sanda na Ijara AP.

An mayar das hi wani Ofis ne da Al-shabab suka kaiwa hari a karshen shekarar da ta wuce. Hakan ya saka shi cikin kunci da matsananciyar damuwa,” a cewar abokan aikin sa.

DUBA WANNAN: Kananan hukumomi biyar da PDP ta bawa APC mamaki a zaben jihar Kaduna

Wani jami’in ‘yan sanda a yankin gabashin Kenya, Mohamud Saleh, ya bayyana cewar sun fara binciken mutuwar dan sandan.

Kafin afkuwar wannan lamari, an dade ba a samu wani rahoto maras dadi da ya shafi ‘yan sanda ba a kasar Kenya kamar yadda hukuma ta sanar.

‘Yan sanda sun bayyana cewar irin wannan lamari na faruwa ne yayin da mutum ke fuskantar matsaloli tsakanin sad a na gaba da shi a wurin aiki ko kuma tsakanin sa da iyalin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel