Idan da arziki da kwanciyar hankali: Karanta rahar da Dangote ya yi ma abokinsa attajiri

Idan da arziki da kwanciyar hankali: Karanta rahar da Dangote ya yi ma abokinsa attajiri

Fitaccen attajirin nan dan asalin jihar Kano, Alhaji ALiko Dangote da wani abokinsa, shima hamshakin attajiri Femi Otedola sun yi ma juna barkwanci a safukansu dake kafar sadarwar zamani ta Twitter, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan raha ta faru ne a daidai lokacin da Dangote ke ma Otedola maraba da shigowa shafin Twitter, inda yace: “Ku taya abokina Femi Otedola murnar shigowa Twitter”

KU KARANTA: Jerin Kamfanoni guda 50 da Najeriya ta baiwa kwangilar hakar danyen mai a shekarar 2018

Idan da arziki da kwanciyar hankali: Karanta rahar da Dangote ya yi ma abokinsa attajiri

Dangote da Otedola

Inda shi kuma Otedola ya mayar masa da martani da cewa: “Nagode abokina, abin koyi a gare ni, kuma babban dan kasuwa daya ciri tuta a nahiyar Afirka.”

Majiyar ta kara da cewa Dangote ya shiga shafin Twitter ne tun a shekarar 2013, yayin da abokin nasa Otedola ya bude nasa shafin a wata Feburairun shekarar 2018, amma bai fara aiki ba sai a shekarar 2018.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel