Mabarata sun yi watsi da goma ta arziki, sun koma bakin aiki a garin Abuja

Mabarata sun yi watsi da goma ta arziki, sun koma bakin aiki a garin Abuja

'Daruruwan mabarata da hukumar kula da zamantakewa ta yashe kuma ta jibge su a cibiyar ladabtar da dan Adam ta garin Bwari, sun koma bakin aiki da fagen sana'ar su ta barace-barace a manyan hanyoyin babban birnin kasar nan.

Kafar watsa labarai ta jaridar The Punch ta ruwaito cewa, mafi akasarin mabaratan da suka kangare suna cin karen su babu babbaka ne a manyan hanyoyi da suka hadar da Zuba zuwa Kubwa, Wuse, Jabi da kuma sassa daban-daban inda suke roke abin hannun al'umma cikin garin Abuja.

Sai dai da yawan mabaratan sun yi koken cewa irin tsauraran dokoki na cibiyar ladabcin ya sanya suka tsere sakamakon rashin sukuni da walwala.

Mabarata sun yi watsi da goma ta arziki, sun koma bakin aiki a garin Abuja

Mabarata sun yi watsi da goma ta arziki, sun koma bakin aiki a garin Abuja

Shugaban hukumar kula da zamantakewa, Nasir Danmallam, ya shaidawa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata cewa, sun yashe kimanin mabarata da marasa matsuguni 861 a tsakani watan Janairu da Afrilun na wannan shekara.

KARANTA KUMA: Wani Makiyayi ya yiwa 'Yar shekara 14 Fyade a jihar Ebonyi

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin wannan adadi hukumar ta jibge mabarata 228 a cibiyar ladabci, inda ta danka sauran a hannu gwamnatin jihohin su da mafi akasarin su 'yan Arewacin Najeriya ne.

Danmallam ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da yadda mabaratan suka yi watsi da wannan goma ta arziki na hukumar, inda ya jaddada cewa nan ba da jimawa ba za su shawo kan wannan kalubale.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel