An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa (hoto)

An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa (hoto)

Yan kwanakin nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Jigawa ziyarar aiki na kwanaki biyu. A lokacin ziyarar, ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar tayi.

An gudanar da wata yar kwarya-kwaryar walima a yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Mayu domin karrama shugaba Buhari, yayinda a ranar Talata, 15 ga watan Mayu aka gudanar da gangami.

Daga cikin ayyukan da shugaba Buhari ya kaddamar kwamitin tsaron jama’a na jihar wanda doka ta samar a kwanakin baya da kuma kamfanin sarrafa abinci a Birnin Kudu.

KU KARANTA KUMA: Bazaku iya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – El-Rufai’i ga tsoffin yan PDP

A lokacin ziyaran an gano shugaba Buhari tare da gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, a gaban wani wajen siyar da kayan marmari.

Ga hoton a kasa:

An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa (hoto)

An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa

A halin da ake ciki Shugaba Buhari ya bayyana cewa aikin da gwamnatinsa tayi da nasarorin da ta samu cikin shekaru uku yafi na adanda sukayi shekaru 16 suna mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel