Gwamnati za tayi wa jihohin da rikici ya shafa wani babban gata, ta ware N10bn

Gwamnati za tayi wa jihohin da rikici ya shafa wani babban gata, ta ware N10bn

- Gwamnatin tarayya ta ware makudden kudade don sake gina garuruwan da suka lalace saboda rikice-rikice

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara sasanin yan gudun hijira a Benue

- Osinbajo kuma ya ce shugaban kasa ya shawarci manoma, 'yan kasuwa da masu sana'o'in hannu su c morayar shirrin bayar da bashi na gwamnatin tarayya

A jiya ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta ware N10 biliyan don sake gina wuraren da suka lalace a sakamakon rikice-rikicen da suka rika faruwa a jihar Benuwe da wasu jihohin Najeriya.

Gwamnati ta ware N10bn don yin gyara a jihar Benuwe da wasu wuraren da rikici ya shafa - Osinbajo

Gwamnati ta ware N10bn don yin gyara a jihar Benuwe da wasu wuraren da rikici ya shafa - Osinbajo

Osinbajo ya bayyan hakan ne yayin da ya kai ziyara sasanin 'yan gudun hijira da ke Abagena da ke hanyar Makurdi-Lafia a yayin da ya kai ziyarar aiki na kwanaki biyu a jihar ta Benuwe.

DUBA WANNAN: Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi

Ya ce bayan ziyarar da shugaba Buhari ya kai jihar a ranar 12 ga watan Maris, shugaban ya bayar da umurin a gudanar da sahihiyar bincike don gano adadin gidaje da gonaki da akayi asarar su saboda a taimakawa wadanda abin ya shafa su dawo gidajensu.

"Shugaban kasa ya bayar da umurnin sake gina duk wuraren da suka lalace ciki har da jihar Benue. An ware N10 biliyan saboda aikin kuma za'a fara gudanar da ayyukan cikin kankanin lokaci saboda ku yan gudun hijira ku samu ko koma gidajenku ku cigaba da rayurwarku," inji shi.

Osinbajo kuma ya ce shugaban kasan ya umurce shi ya tunatar da 'yan kasuwa, manoma da masu sana'o'in hannu suyi amfani da damar da gwamnati ta bayar da bada basusuka kamar na 'anchor borrowers' don bunkasa ayyukansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel