Tattalin arziki: Shugaba Buhari yayi wa mutanen Jigawa albishir

Tattalin arziki: Shugaba Buhari yayi wa mutanen Jigawa albishir

- Shugaba Buhari yace tattalin arzikin Najeriya ya mike

- Tsadan kayan masarufi na raguwa matuka a Najeriya

- Haka kuma darajar Naira na dai dawowa a halin yanzu

Bisa dukkan alamu abubuwa sun kama hanyar yin kyau a Najeriya. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘Yan Najeriya albishir da cewa tattalin kasa na mikewa a Gwamnatin sa. Buhari ya bayyana wannan ne shekaran jiya a Jigawa.

Tattalin arziki: Shugaba Buhari yayi wa mutanen Jigawa albishir

Shugaba Buhari ya kai ziyara Jihar Jigawa a makon nan

Shugaban Kasa Buhari yace abubuwa za su kara yin kyau nan gaba a Najeriya ganin yadda tattalin arzikin na Najeriya ke cigaba da habaka. A halin yanzu dai kudin kasar wajen da Najeriya ta mallaka kusan ya ribanya abin da ta samu.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kashe Tiriliyan 1.5 wajen ayyukan gina kasa

Asusun Najeriya na kudin kasar waje sai dai yayi kasa da Dala Biliyan $28. Yanzu dai Najeriya na da kusan Dala Biliyan $50. Bayan nan dai Shugaban kasar yace Naira ta kara daraja bayan ta sha kasa a baya a farkon Gwamnatin nan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa alkaluman da aka fitar a makon nan sun nuna cewa kayan masarufi na rage tsada a Najeriya. Bugu-da-kari kuma masu hannun jari daga Kasar waje sun fara zuba kudin su a Najeriya a yanzu.

Hakan dai na nufin tattalin arzikin kasar zai bunkasa sannan kuma jama’a za su samu aikin yi bayan kuma saukin kaya da za a samu a kasuwa. A baya dai tattalin arzikin Najeriya ya ruguje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel