An hurowa Amurka wuta ta binciki wani na hannun-daman Bukola Saraki

An hurowa Amurka wuta ta binciki wani na hannun-daman Bukola Saraki

Mun samu labari daga Abu Sidiqu cewa wata Kungiya mai zaman kan-ta mai suna HEDA a kasar waje tayi kira ga Gwamnatin Amurka ta binciki Bamikole Omishore wanda yana cikin ba Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki shawara.

Mr Olanrewaju Suraju shi ne Shugaban wannan Kungiya ta HEDA ya nemi ayi bincike game da zargin badakalar da ke kan wuyan Mista Bamikole Omishore wanda ke ba Bukola Saraki shawara kan harkokin kasashen waje.

An hurowa Amurka wuta ta binciki wani na hannun-daman Bukola Saraki

Matar Omishore tana cin albashi ne da wani suna Abiola Joy Aiyegbayo

Ana tunani ma Hukumar EFCC za ta fara binciken zargin da ake yi na cewa Bamikole Omishore ya sa sunan Mai dakin sa Abiola Aiyegbayo-Omishore cikin masu aiki da Bukola Saraki duk da cewa tana can Kasar Amurka a kwance.

Abiola Aiyegbayo-Omishore tana aiki ne a wani asibiti a Kasar Amurka amma kuma tana karbar kudi akalla N150, 000 duk wata daga Majalisar Kasar. Misis Abiola Omishore tana karbar kudin ne ta wani akawun din ta a bulis.

KU KARANTA: An taso Shugaban Hukumar EFCC Magu a gaba

Bayan Mai dakin ta sa dai ana tunanin Hadimin na Saraki yana amfani da Ma’aikatan bogi iri-iri yana lashe kudi daga Majalisar Dattawa. Bincike ya nuna cewa tun 2015 dai Iyalin Hadimin Sarakin ta ke cin kudi duk da ba ta aiki.

Yanzu dai an huro wuta Gwamnatin Kasar Amurka tayi ram da Abiola aiyegbayo- Omishore saboda wannan badakala. HEDA tace Matar mai ba Shugaban Majalisar Dattawan shawara ba ta taba aiki a Najeriya ba amma tana karbar albashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel