Ba mu halarci taron bude ofishin Jakadancin Amurka a Kudus ba – Gwamnatin Najeriya

Ba mu halarci taron bude ofishin Jakadancin Amurka a Kudus ba – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta musanya cewa tana cikin Kasashen da su ka halarci bikin taron maida ofishin Jakadancin Amurka a Kasar Israila zuwa Garin Kudus watau Jerusalem.

An rahoto cewa Najeriya da wasu Kasashen Afrika har kusan 10 sun halarci wannan taro a Ranar Litinin. Sai dai mun samu labari daga wasu manya a Gwamnatin Najeriya cewa karya ne sam Kasar ba ta cikin wadanda aka yi wannan biki da ita.

Wani babban Jami’i a Gwamnati da ya ki bayyana sunan sa ya bayyanawa Jaridar Vanguard cewa Najeriya ba ta aika wakilin ta ba wajen wannan taro. Gwamnatin Kasar ta nemi a cire sunan ta daga cikin wadanda su ka je wajen wannan biki.

KU KARANTA: Real Madrid za ta biya wa Ronaldo taran da ke kan sa

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ne ya dauki wannan danyen mataki na dauke Jakadancin Amurka daga Birnin Tel Aviv zuwa Birnin Kudus wanda hakan ya kawo rikici a Yankin. An dai yi zanga-zanga har ta kai wasu da dama ma sun mutu.

Wani daga cikin Hadiman Shugaban kasar dai ya tabbatar da cewa babu Najeriya cikin masu goyon bayan wannan aiki na Shugaban Amurka. Tuni dai har Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya aikawa Jakadan Najeriya ya zo yayi masa bayani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel