Wani Makiyayi ya yiwa 'Yar shekara 14 Fyade a jihar Ebonyi

Wani Makiyayi ya yiwa 'Yar shekara 14 Fyade a jihar Ebonyi

Mun samu rahoton cewa wani makiyayi na Fulani da aka sakaya sunan sa ya fyade wata budurwa ‘yar shekaru 14 da haihuwa a yankin Umuifi dake garin Anioma a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.

A halin yanzu wannan dalibar sakandiren na karbar kulawa ta kwararrun lafiya a wani asibiti kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Shugaban wannan yanki, Festus Nwachukwu ya bayya cewa, tuni dai wanda ya aikata wannan aika-aika ya shiga hannun jami'an tsaro na ‘yan sanda.

Wani Makiyayi ya yiwa 'Yar shekara 14 Fyade a jihar Ebonyi

Wani Makiyayi ya yiwa 'Yar shekara 14 Fyade a jihar Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan makiyayi ya yiwa budurwar ta karfi ne a gonar su tana tsaka da aiki bayan da ya nuna mata ‘yan kudaden sa na N700 da ya yi alkawarin sun zama mallakin ta muddin ta amince da bukatar sa.

KARANTA KUMA: Yadda Kindirmo ke Maganin Ciwon Asma da Kumburin Gabbai

A wannan yanayi budurwa ta ce kafa mai na ci ban baki ba, inda kafin ta yi wani dogon taku ya cimmata kuma ya aikata alfashar da ya nufata.

Sai dai a yayin tuntubar kakakin ‘yan sanda na jihar, ASP Loveth Oda, ya bayyana cewa ba ya da tabbaci akan wannan rahoto inda ya sha alwashi na bankado tushen rahoton.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel