Nigerian news All categories All tags
Komai cancantar ka idan ba ka da kudi a siyasa ka yi banza – Shehu Sani

Komai cancantar ka idan ba ka da kudi a siyasa ka yi banza – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya tubewa ‘yan siyasar kasar nan zani

- ‘Dan Majalisar yace idan har ‘Dan takara bai da kudi ya fadi

- Shehu Sani dai yace ana barna wajen zaben fitar da gwani

Sanata Shehu wanda ba yau ya saba fitowa yayi magana kan abubuwan da su ka shafi kasa ba ya fito yayi magana game da irin barnar da ake tafkawa kafin mutum ya iya tsayawa takara a Najeriya.

Komai cancantar ka idan ba ka da kudi a siyasa ka yi banza – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace sai da kudi ake iya tsayawa takara

Shehu Sani wanda shi ne ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya bayyana cewa kafin Jam’iyya ta tsaida mutum takara sai ya biya makudan kudi. Sanatan yace masu kudi ne kurum ke iya samun tikitin Jam’iyya.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna El-Rufai ya maidawa 'Yan N-PDP martani

Sanatan na Jam’iyyar APC a bayanin da yake yi a shafin sa na Tuwita yace duk yadda ‘Dan takara ya kai ya kawo wajen cancanta, da zarar bai da kudin da zai biya masu fitar da gwani, to babu shakka za ayi babu shi kuwa.

Fitaccen ‘Dan Majalisar yace ‘Yan siyasa na gudun yi maganar irin barnar da ake yi wa wajen zaben fitar da ‘Dan takarar Jam’iyya. Sanatan dai a wani jawabi da yayi dabam yace ya yarda cewa Shugaba Buhari ya cika mai gaskiya.

Kun ji cewa wani Bawan Allah mai suna Aliyu Tilde wanda ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ya bayyana muradun sa. Dr. Tilde yace ba zai karbi makudan alawus ba in ya zama Sanata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel