Nigerian news All categories All tags
Magu ya sha caccaka a wurin matasan jam’iyyar PDP saboda saka hoton takarar Buhari

Magu ya sha caccaka a wurin matasan jam’iyyar PDP saboda saka hoton takarar Buhari

Wasu matasan jam’iyyar PDP karkashin wata kungiya (PDPNYF) ta caccaki mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, bisa makala hoton takarar Buhari a jikin rigar sa.

Magu ya bayyana a wani shiri na gidan Talabijin din Channels a yau makale da wani hoton takarar shugaba Buhari a jikin rigar sa.

Matasan jam’iyyar ta PDP sun bayyana, a shafin sun a Tuwita, cewar Magu ya tabbatar da cewar shi dan jam’iyyar APC ne tunda ya saka abin kamfen din dan takarar jam’iyyar.

Magu ya sha caccaka a wurin matasan jam’iyyar PDP saboda saka hoton takarar Buhari

Buhari da Magu

A cewar matasan, bai kamata shugaban wata hukumar gwamnati mai zaman kan ta ya zama mai nuna ra’ayin wata jam’iyyar siyasa ba.

Kazalika matasan sun bayyana cewar, makala hoton da Magu ya yi ya tabbatar da zargin da wasu keyi na cewar yaki da cin hancin hukumar EFCC ya jirge bangaren jam’iyyar adawa ne.

DUBA WANNAN: PDP Ta bawa APC mamaki a wasu kananan hukumomi a zaben jihar Kaduna

A yau ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta koma sabon ofishin ta da aka kashe biliyan N24bn wajen gina shi. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon ofishin.

Mai rikon kwaryar shugabancin hukumar, Ibrahim Magu, ya bayyana jin dadin sa bisa kammala aikin ginin sabuwar shelkwatar hukumar.

"Ina godiya ga shugaban kasa da ya bawa wannan aiki fifiko. Hakan ya kara jadda aniyar da yake da ita ta yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Wannan gagarumin aiki ne da zai saka Najeriya alfahari da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel