Nigerian news All categories All tags
Irin kokarin da mu ke yi a Gwamnatin nan – Inji Ministar Buhari

Irin kokarin da mu ke yi a Gwamnatin nan – Inji Ministar Buhari

Ministar kudi ta Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari watau Kemi Adeosun ta bayyana cewa a shekarar nan an kashe abin da ba a taba kashewa ba wajen gina abubuwan more rayuwa a Najeriya.

Kemi Adeosun da ta ke wani jawabi kwanaki a shafin ta na Tuwita, ta bayyana cewa an kashe abin da ya haura Naira Tiliyan 1.5 daga cikin kasafin kudin shekarar bara na 2017 wajen gina tituna da kuma sauran abubuwan gina kasa.

Irin kokarin da mu ke yi a Gwamnatin nan – Inji Ministar Buhari

Ministar Buhari tace su na jiran kasafin kudin bana

Kusan dai a tarihi ba a taba samun Gwamnatin da ta ware tsantsagoron kudi wajen ayyukan gina kasa irin wannan Gwamnati ba. Adeosun tace abin da aka kashe a bana ya ma zarce abin da aka kashe a kasafin kudin shekarar 2016.

KU KARANTA: El-Rufai yace babu wanda ya isa ya hana Buhari zarcewa

A shekarar nan Ministar tace an samu karin kudin shiga ta hanyar haraji saboda irin kokarin da su ka yi. Ministar har wa yau ta ke cewa su na jira ne Majalisa tayi maza ta amince da kasafin kudin wannan shekarar domin a cigaba da aiki.

A makon nan ne ake sa rai za a amince da kasafin kudin wannan shekarar ta 2018 bayan sama da wata 6 ana jiran Majalisa ta kammala aiki a kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel