Nigerian news All categories All tags
Kalli yadda Buhari ya kirga makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

Kalli yadda Buhari ya kirga makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

A wani irin lamari da ba kasafai aka saba ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, a yau Talata 15 ga watan Mayu, an hange shi a sabon shelkwatar hukumar yaki da rashawa, EFCC yana kirgar kudade, inji rahoton jaridar the Cable.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bayan kammala bikin bude sabon ofishin na EFCC, sai shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya jagoranci tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da manyan baki da aka gayyata zuwa zagayen gani da ido a shelkwatar.

KU KARANTA: Azumin watan Ramadana: An yi kira ga Malamai game da zage zage yayin fassara Al-Qur’ani

Kalli yadda Buhari ya kirge makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

Buhari

A yayin zagayen aikin ne sai aka nuna ma Buhari wasu makudan daloli da hukumar ta kwato daga hannun barayin gwamnati, inda ya dauki bandir guda na kudin ya fara kirgawa, hakan ya sanya jama’an dake wajen fashewa da dariya suna mamakinsa.

Daga cikin wadanda suka take ma shugaba Buhari baya akwai sakataren gwamnati, Boss Mustapha, Kaakakin majalisa Yakubu Dogara, tsohon shugaban kasar Afirka ta kudd Thabo Mbeki, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefelie da sauran manyan baki.

Kalli yadda Buhari ya kirge makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

Buhari

Wannan sabon ofishi dai an fara gininsa ne tun a zamanin tsohuwar shugaban hukumar, Farida Waziri, inda aka kashe makudan kudade da suka kai naira biliyan ashirin da biyar, 25,000,000,000.

Kalli yadda Buhari ya kirge makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

Buhari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel