Nigerian news All categories All tags
Bazaku iya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – El-Rufai’i ga tsoffin yan PDP

Bazaku iya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – El-Rufai’i ga tsoffin yan PDP

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I, yace koda tsofaffin ‘yan PDP na arewa sun bar jam’iyyar APC bazai hana shugaba Muhammadu Buari samun nasarar zabe ba a 2019

- El-Rufa’I yace tun shekarar 2003, Buhari yana cin zabe a jihohin Kwara, Adamawa, Kano da Sokoto, inda yawancin ‘yan PDP arewa suka fito

- Kungiyar sun kalubalanci ciyaman na jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, sun kumayi koyi da shugaba Buhari a cikin dattawan jam’iyyar

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, yace koda tsofaffin ‘yan PDP na arewa sun bar jam’iyyar APC bazai hana shugaba Muhammadu Buari samun nasarar zabe ba a 2019.

El-Rufai'i yace tun shekarar 2003, Buhari yana cin zabe a jihohin Kwara, Adamawa, Kano da Sokoto, inda yawancin ‘yan PDP arewa suka fito, ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema abarai na gidan gwamnati.

Bazaku iya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – El-Rufai’i ga tsoffin yan PDP

Bazaku iya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – El-Rufai’i ga tsoffin yan PDP

Kungiyar sun kalubalanci ciyaman na jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, sun kumayi koyi da shugaba Buhari a cikin dattawan jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Matasa kuna batawa kanku lokacin ne idan har baku da katin zabe a 2019 - Utomi

A ranar 27 ga watan Afirilu ne suka rubuta takardar kalubalen ga jam’iyyar ta APC, tare da sanya hannun ciyaman na kungiyar Abubakar kawu Baraje da sakataren Kungiyar Olagunsoye Oyipetition, wanda a ranar Laraba, suka jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa sakatariyar jam’iyyar APC, inda suka bayar da wa’adin kwanaki bakwai na ganin shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel