Nigerian news All categories All tags
Rikicin jihar Benuwe: Mataimakin shugaban kasa ya isa Makurdi don ganawa da yan gudun hijira

Rikicin jihar Benuwe: Mataimakin shugaban kasa ya isa Makurdi don ganawa da yan gudun hijira

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya isa garin Makurdi na jihar Benuwe a wani ziyarar aiki, inda zai kwashe kwanaki biyu yana ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar don gano bakin zaren game da kashe kashen da ya dabaibaye jihar.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito Osinbajo ya samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jihar Samuel Ortom, ministan harkokin noma, Audu Ogbeh, shugaban hukumar bada agajin gaggawa Mustapha Maihaja da sauran wasu jami’an gwamnati.

KU KARANTA: Rikicin Duniya da mai rai ake yinta: Majalisa ta gayyaci Sanatoci biyu kan bahallatsar satar sandan iko

Rikicin jihar Benuwe: Mataimakin shugaban kasa ya isa Makurdi don ganawa da yan gudun hijira

Osinbajo

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana sa ran Osinbajo zai ziyarci sansanonin yan gudun hijira dake Abagana, Gbajimba da Anyi, inda zai tattauna da yan gudun hijiran kan matsalolin da suke fuskanta.

Rikicin jihar Benuwe: Mataimakin shugaban kasa ya isa Makurdi don ganawa da yan gudun hijira

Osinbajo

Jihar Benuwe dai ta sha fama da matsalolin tsaro da ya faro kamar rikicin manoma da makiyaya, amma daga bisani ya zama wani abu na daban, inda aka kashe daruruwan mutane da suka hada da Musulmai, Kiristoci, Fulani, Tibi da sauran kabilu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel