Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin jihar Kaduna ta tasa keyar Zakzaky gaban Kotu kan zargin tada zauni tsaye

Gwamnatin jihar Kaduna ta tasa keyar Zakzaky gaban Kotu kan zargin tada zauni tsaye

Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da shugaban yan Shi’a na Najeriya, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa kan zarginsa da tada zauni tsaye, a gaban babbar Kotun jihar Kaduna, inji rahoton gidan talabijin na Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin jihar Kaduna na tuhumar Zakzaky akan laifuka guda takwas, da suka hada da kisah kai, gudanar da taro ba akan ka’ida ba, tayar da hankulan jama’a da dai sauransu.

KU KARANTA: Abin takaici: Yadda wani Magidanci ya dirka ma diyarsa mai shekaru 15 ciki a jihar Gombe

Gwamnatin jihar Kaduna ta tasa keyar Zakzaky gaban Kotu kan zargin tada zauni tsaye

Zakzaky

Jami’an hukumar tsaro na sirri, DSS ne suka dauko Zakzaky da matarsa Zeenatu, tun daga babban birnin tarayya Abuja zuwa garin Kaduna cikin wasu manyan motocin SUV guda biyu, zagaye da tsatstsauran tsaro.

A zaman kotun, lauyan Zakzaky, Maxwell Kyon ya bayyana ma Kotun cewar a saki wanda yake karewa sakamakon sama da shekaru biyu kenan suke daure a hannun gwamnati, sai dai Alkalin kotun, mai shari’a Kurada ya yi watsi da bukatar da Lauyan, inda ya bukaci ya mika bukatarsa a rubuce.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tasa keyar Zakzaky gaban Kotu kan zargin tada zauni tsaye

Zakzaky

Daga nan kuma sai Alkalin y adage sauraron karar zuwa ranar 32 ga watan Yuni. Tun a watan Disamnar shekarar 2015 ne dai gwamnatin Najeriya ta kama Zakzaky, wanda hakan ya sanya mabiyansa gudanar da zanga zanga akai akai a Abuja.

Don ko a ranar Talata 15 ga watan Mayu da ya bayyana a gaban Kotu sai da mabiyansa suka tare babban titin AHmadu Bello dake garin Kaduna, har zuwa Kotun da ake sauraron karar shugaban nasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel