Nigerian news All categories All tags
Matasa kuna batawa kanku lokacin ne idan har baku da katin zabe a 2019 - Utomi

Matasa kuna batawa kanku lokacin ne idan har baku da katin zabe a 2019 - Utomi

- Farfesa Pat Utomi, ya bukaci matasan Najeriya da suyi amfani da damarsu ta katin zabe su canza gwamnatin zuwa wadda sukeso

- Utomi yayi kiran ga matasan a ranar Talata, a jihar Legas, inda ya bukaci matasan da suje suyi katin zabe tun kafin lokacin zaben na 2019 yazo

- Utomi yace zabe shine kawai karfin da talaka yake dashi na canza gwamnati idan har yaga bata biya masa bukatarsa ba

Farfesa Pat Utomi, ya bukaci matasan Najeriya da suyi amfani da damarsu ta katin zabe su canza gwamnatin zuwa wadda sukeso.

Utomi yayi kiran ga matasan a ranar Talata, a jihar Legas, inda ya bukaci matasan da suje suyi katin zabe tun kafin lokacin zaben na 2019 yazo.

Matasa kuna batawa kanku lokacin ne idan har baku da katin zabe a 2019 - Utomi

Matasa kuna batawa kanku lokacin ne idan har baku da katin zabe a 2019 - Utomi

Utomi yace zabe shine kawai karfin da talaka yake dashi na canza gwamnati idan har yaga bata biya masa bukatarsa ba, saboda haka ya zama dole matasa su dage don ganin cewa an gina kasar da kuma nada shuwagabanni na kwarai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tashin bam ya kashe mutane 5 a wani gari dake jihar Borno

Ya kara da cewa yanzu lokaci yazo da matasa ya kamata su karbi mulki da jagorancin siyasar Najeriya da kuma gwamnatin kasar baki daya. Saboda haka ya bukaci matsa da dage wurin ganin sun samu katin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel