Nigerian news All categories All tags
Ba zan baku kunya – Buhari ga yan Najeriya

Ba zan baku kunya – Buhari ga yan Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana cewa gwamnatinsa bazata bawa ‘yan Najeriya kunya ba, yace ana iyaka kokari don ganin an magance wahalhalun da suke fuskanta

- Buhari ya bayyana hakan ne a wurin taron siyasa a garin Dutse na jam’iyyar APC, a mtasayin daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar yaje yi a jihar ta Jigawa

-Buhari yace yana sane da tsananin da mutanen kasa ke fuskanta sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsadar kayayyakin masarufi

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 15 ga watan Mayu, 2018, ya bayyana cewa gwamnatinsa bazata bawa ‘yan Najeriya kunya ba, yace ana iyaka kokari don ganin an magance wahalhalun da suke fuskanta.

Buhari ya bayyana hakan ne a wurin taron siyasa a garin Dutse na jam’iyyar APC, a mtasayin daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar yajeyi a jihar ta Jigawa.

Ba zan baku kunya – Buhari ga yan Najeriya

Ba zan baku kunya – Buhari ga yan Najeriya

Buhari yace yana sane da tsananin da mutanen kasa ke fuskanta sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsadar kayayyakin masarufi, yace gwamnatin tarayya ta hana shigowa da shinkafa ne domin ta karawa manoman shinkafar na gida kwarin gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tashin bam ya kashe mutane 5 a wani gari dake jihar Borno

Gwamnan jihar ta Jigawa Muhammadu Badaru ya bayyanawa mutanen jihar cewa shugaban kasar yana iyaka gwargwadon kokarinsa don magance matsalolin ‘yan Najeriya, duk da cewa tattalin arzikin kasar ya lalace a lokacin da shugaba Buhari ya karbi mulkin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel