Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kada ya saurarawa Barayi

Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kada ya saurarawa Barayi

- Ya kamata dakunan sabon makeken shelkwatar hukumar EFCC su cika da tsoffin barayin shugabannin Najeriya a cewar Soyinka

- Domin dakunan zasu yi kyau da su har sai sun amayo kudaden da suka sace

Shahararran Marubucin nan mai lambar girmamawa ta Nobel Laureate Farfesa Wole Soyinka yayi kira ga shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) Ibrahim Magu da kada ya saurarawa Barayin gwamnati.

Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kaad ya saurarawa Barayi

Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kaad ya saurarawa Barayi

A cewarsa yaki da cin hanci da rashawa ba zai samu cikakkiyar nasara ba har sai idan tsagin shari’a sun bi sahun hukumar.

Soyinka ya shaida hakan ne a yayin taron shugabannin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasashe takwas a Nahiyar Africa rainon Ingila.

KU KARANTA: Ba zan baku kunya – Buhari ga yan Najeriya

Sannan ya bayyana mamakinsa lokacin da ya tambayi Magu ko ina dakin da za’a tsare shugabanni idan an kamo su, maimakon yaga daki mai kyau sai kawai ya gan shi gashi ga kamarsa.

A cewarsa duk shuwagabanni masu cin hanci sai su shirya don zasu shiga dakunan da aka gina na humakar

Marubucin ya kuma bayyana cewa shi ba Mutum ne mai burin daukar fansa ba, amma lallai ya kamata a ce wasu daga cikin shuwagabannin da suka mulki Najeriya sun ziyarci sabbin dakunan.

Kuma duk yunkurin hukumar ba zai kai ga gaci ba mutukar ‘yan bangaren shari’a ba su shigo tsarin anyi da su ba.

Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kaad ya saurarawa Barayi

Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kaad ya saurarawa Barayi

Ya kuma kara da cewa “A yanzu babban abinda yake gaban hukumar ta EFCC shi ne kwato dukiyar da aka sace ta kasar nan.”

A nasa jawabin babban Mai Shari’a na kasar nan Walter Onnoghen, ya bayyana taron amatsayin hanyar da zai bawa shuwagabannin hukumomin yaki da cin hanci da rashawar damar aiki tare da kuma fahimtar yadda sauran kasashen suke bi don zurfafa bincike da magance matsalolin a nasu kasashen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel