Nigerian news All categories All tags
Rikicin Duniya da mai rai ake yinta: Majalisa ta gayyaci Sanatoci biyu kan bahallatsar satar sandan iko

Rikicin Duniya da mai rai ake yinta: Majalisa ta gayyaci Sanatoci biyu kan bahallatsar satar sandan iko

Kwamitin hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da majalisar wakilai da hakkin binciken musabbabin satar sandan iko na majalisar dattawa ya rataya a wuyansu sun gayyaci wasu manyan Sanatoci guda biyu, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin ta bayyana sunayen Sanata Ovie Omo-Agege da Sanata Ali Ndume, dukkaninsu yayan jam’iyyar APC, a matsayin mutanen da ake zargi da shirya satar sandar ikon da aka yi a ranar 18 ga watan Afrilu, don haka ta bukaci su gurfana a gabanta.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram a wani mummunan samame da suka kai

Rikicin Duniya da mai rai ake yinta: Majalisa ta gayyaci Sanatoci biyu kan bahallatsar satar sandan iko

Ali Ndume da Omo Agege

Shugaban kwamitin, Sanata Bala Ibn Na-Allah ne ya sanar da sammacin ga Sanatocin biyu, a yayin zaman kwamitin a ranar Talata 15 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja, inda bayanai daga shuwagabannin hukumomin tsaro dake jibge a majalisar sun nuna cewa Omo Agege ne ya shigar da barayin cikin farfajiyar majalisar.

Haka zalika Na-Allah ya bayyana cewa sun gano cewar Sanata Ndume ne ya hana shugaban dogarawan majalisar boye sandan ikon a inda ya kamata, inda yace: “Duba da bayanan shugaban Dogarawan majalisa, kai ne ka hana a baiwa sandar tsaro. Don haka ga gurfana a gaban Kwamitin.”

Rikicin Duniya da mai rai ake yinta: Majalisa ta gayyaci Sanatoci biyu kan bahallatsar satar sandan iko

Satar sandan iko

Daga karshe Na Allah ya umarci sanatocin biyu da su gurfana a gaban kwamitin a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu da misalin karfe 11 na safe, sa’annan ya aika da wasikar sammacin ga Sanatocin.

A satin data gabata ne dai shugaban Yansanda dake gadin majalisun dokokin Najeriya, Sulu-Gambari Abdul yayi zargin cewa wasu Sanatoci ne suka hada baki da barayin wajen afkawa cikin majalisa har ta kai ga an sace sandan iko.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

https://www.youtube.com/watch?v=4nD0mwh8Yp4

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel