Nigerian news All categories All tags
Da dumin sa: ‘Yan sanda sun tabbatar da kama mabiya Shi’a 60

Da dumin sa: ‘Yan sanda sun tabbatar da kama mabiya Shi’a 60

Hukumar ‘yan sandan Najeriya reshen Abuja ta tabbatar da kama mambobin kungiyar ‘yan uwa musulmi (IMN) da fi sani da Shi’a, 60 bayan barkewar rikici yayin gudanar da zanga-zanga a Abuja, jiya, Litinin.

Magoya bayan Shi’a sun yi watsi da gargadin hukumar ‘yan sanda tare da gudanar da zanga-zangar neman a saki shugaban su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, dake tsare a hannun hukuma tun shekarar 2016.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a Abuja, Anjuguri Manzah, ya tabbatar da kama ‘yan shi’ar yayin wata ganawa da manema labarai yau, Talata, a asibitin Garki dake Abuja.

Manzah ya je asibitin ne domin duba lafiyar jami’an ‘yan sanda da suka samu raunuka yayin kokarin tarwatsa masu zanga-zangar a jiya.

Da dumin sa: ‘Yan sanda sun tabbatar da kama mabiya Shi’a 60

Mabiya Shi’a

Jami’an da suka samu raunukan sune; Linus Ogah, mai mukamin SP, day a samu rauni a fuska hart a kai baya iya bude idanuwan sad a kuma Mary Ameh, mai mukamin Insifekta, da ta samu rauni a daya daga cikin hannayen ta.

Kakakin hukumar ;yan sandan y ace an cire harsashi daga hannun ‘yar sanda Umeh, ya kara da cewa masu zanga-zangar sun lalata wasu motocin ‘yan sanda.

DUBA WANNAN: Matar dan siyasa tayi barin juna biyu a hannun 'yan sanda, an bayar da ita beli bayan wata guda

Ko a ranar 16 ga watan Afrilu saida jami’an ‘yan sanda suka kama mabiya Shi’a 60 bisa laifin gudanar da zanga-zangar neman sakin Zakzaky a Abuja.

Mista Manzah, wanda ya ce dukkan ‘yan kasa na da ‘yancin gudanar da zanga-zanga, ya bayar da shawara ga ‘yan Najeriya cewa kada zanga-zanga ta rikide zuwa rikici ko kuma tayar da tsugune tsaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel