Nigerian news All categories All tags
Sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram a wani mummunan samame da suka kai

Sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram a wani mummunan samame da suka kai

Dakarun askarawan rundunar Sojin kasa sun samu wata muhimmiyar galaba akan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, a wani hari da yayi kama da na mayar da biki.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar, Birgediya Texas ne ya sanar da haka a ranar Talata, 15 ga watan Mayu, inda yace Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a karkashin aikin Operation Lafiya Dole sun mayar da biki akan yan ta’adda a kauyen Gashigar.

KU KARANTA: Wani Magidanci ya watsa ma Uwargidarsa tafasashshen talge, ko me ya yi zafi?

Texas yace yan ta’addan ne suka fara far ma Sojojin, inda Sojojin ma basu yi kasa a gwiwa ba, suka mayar da biki nan take, ai kuwa cikin ikon Allah suka hallaka yan ta’adda guda shida, tare da jikkata da dama da suka tsere da raunuka.

Sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram a wani mummunan samame da suka kai

Sojojin Najeriya

Bugu da kari Kaakakin yace a sakamakon harin, Sojoji sun kwato bindigu kirar AK 47 guda hudu, Babban bindigar baro jirage, alburusai da dama, bamabamai da kuma motar mai dakon bindiga.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewar Sojoji guda biyu sun samu rauni a yayin karanbattar, inda a wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun samu nasarar kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Gambori, Dumbuwa, Damsu, Awardi, Kanaram, Laridi, Malumdi da Yuramdi.

A sakamon fatattakar yan ta’addan tare da kashe na kashewa, Sojojin sun gano na’urar sanyaya ruwa, Talabijin inci 14, DVD, da wani kwati makare da magunguna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel