Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa (Hotuna)

Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa (Hotuna)

A wani samame da dakarun rundunar Sojin kasa suka a yayin da suke aikin sintiri a kauyen Ugya dake cikin karamar hukumar Toto na jihar Nassarawa, sun samu nasarar tarwatsa wani sansanin yan bindiga tare da kama shugaban yan bindigan.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Sojan kasa, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Talata 15 ga watan Mayu, inda yace rundunar ta 177 ne ta samu wannan nasara, inda ta lalata sansanin gaba daya.

KU KARANTA: Son zuciya bacin zuciya: Wani Baban bola ya fuskanci hukuncin Kotu kan satar karfen rodi

Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa (Hotuna)

Shugaban yan bindigar

Bugu da kari Kaakaki Texas ya bayyana cewar Sojojin sun samu nasarar cafke shugaban kungiyar yan bindigan, wani tsoho mai suna Angulu Idaku, wanda shi ne ke baiwa yan bindigan tsafe tsafen samun sa’a.

Haka zalika yace daga cikin abubuwan da Sojoji suka gano akwai bindigu guda bakwai, alburusai da dama, wukake hudu, adduna goma sha biyar, wayoyin salulu guda shida, Dikodar DSTV da kuma na’urar bada wuta da hasken rana.

Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa (Hotuna)

Makamai

Daga karshe sanarwar ta kara da yin kira ga jama’a da su cigaba da bayyana ma jami’an tsaro ayyukan duk wani mutumin da basu gamsu da take takensa ba.

Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa (Hotuna)

Alburusai

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel