Nigerian news All categories All tags
Bamu san cin hanci ba lokacin da nayi mulki - Gowon

Bamu san cin hanci ba lokacin da nayi mulki - Gowon

A jiya Litnin ne tsohon shugaban kasan mulki soji na Najeriya, Janar Yakubu Gowon (murabus) ya ce a zamanin mulkinsa na tsawon shekaru tara, gwamnatinsa bata yi karo da wani abu wai ci cin hanci ba.

Gowon wanda ya yi mulki daga 1966 zuwa 1975 ya furta wannan magana ne a taron shugabanin hukumomin yaki da cin hanci na shiyoyin nahiyar Afrika karo na takwas wanda hukumar EFCC ta Najeriya ta shirya a Abuja.

Tsohon shugaban kasan ya ce duk da cewa wasu daga cikin ministocinsa sun fuskancin zargin rashawa, gwamnatinsa ta tabbatar cewa babu wanda ya samar damar aikatan cin hancin.

Bamu san cin hanci ba lokacin da nayi mulki - Gowon

Bamu san cin hanci ba lokacin da nayi mulki - Gowon

KU KARANTA: An sake dage sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta

"Ina tabbatar maka cewa a zamaninmu bamu san abinda ake kira cin hanci ba.

"Babu shakka, an zargi wasu daga cikin ministoci na da cin hanci amma munyi kokari mun tabbatar cewa babu wanda ya aikata hakan musamman cikin ma'aikatan gwamnati.

"Lokacin da na sauka daga mulki a 1975, bayan albashi ne da na karba babu wani abu da na mallaka sai kuma wasu ma'aikatan da na hadu da su a taron hadin kan kasashen Afirka (OAU) a Kampala na kasar Uganda da suka yi min karo-karo na dan samu abinda zan lalaba rayuwata dashi," inji shi.

Gowon kuma ya ce ransa na baci bisa irin rahotannin da ya ke ji a kafafen yadda labarai inda ake zargin cewa dukkan tsaffin shugabanin Najeriya sun tafka cin hanci, ya ce hakan na gusar da darajar kujerar mulkin kasar.

Gowon ya yi kira ga 'yan Najeriya su tabbatar wadanda suka zaba suna yi musu adalci kana ya bukaci mahalarta taron su bullo da hanyoyin da zasu hana satar kudaden gwamnati da kuma karbo wandanda ake boye a kasashen waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel