Toh! Wa ya aikata wannan: Najeriya ta yi amanna da mayar da ofishin Jakadancin Amurka Birnin Kudus

Toh! Wa ya aikata wannan: Najeriya ta yi amanna da mayar da ofishin Jakadancin Amurka Birnin Kudus

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Isra’ila ta fitar da jadawalin kasashen da suka samu halartan taron bude sabon ofishin jakandancin kasar Amurka da aka gina a birnin kudud duk da cewa majalisar dinkin duniya da manyan kasashe irinsu Jamus, Faransa a Ingila sun soki hakan.

Abin mamakin shine, an samu sunan Najeriya cikin kasashen da suka tura wakilai taron bude sabuwar ofishin jakadancin.

Jadawalin ya nuna cewa kasashe 33 ne suka halarci wannan taron da ya sabbaba kisan Falasdinawa ba gaira ba dalili.

Toh! Wa ya aikata wannan: Najeriya ta yi amanna da mayar da ofishin Jakadancin Amurka Birnin Kudus

Toh! Wa ya aikata wannan: Najeriya ta yi amanna da mayar da ofishin Jakadancin Amurka Birnin Kudus

A jerin kasashen:

Najeriya, Jamhuriyar Dominican, El Salvador, Itopiya, Jojiya, Guatemala, Honduras, Hungary, Kenya, Myanmar, Albaniya, Angola,Ostiriya, Kamaru, Kongo, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Ivory Coast, Sudan ta Kudu, Tailan, Yukren, Vietnam, Paraguay, Tanzaniya da Zambiya, Jamhuriyar Chek, Masidoniya, Panama, Peru, Filifins, Romaniya, Ruwanda, Sabiya.

KU KARANTA: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su gama da ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

Akalla Falasdinawa 60ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya barke tsakanin Falasdinawa masu zanga-zanga da kuma jami’an sojin Isara’la.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel