Da dumi-dumi: Majalisar tarayya tayi kari kan kasafin kudin 2018

Da dumi-dumi: Majalisar tarayya tayi kari kan kasafin kudin 2018

Majalisar tarayya tayi kari a kan kasafin kudin shekarar 2018 daga triliyan N8.612 zuwa triliyan N9.120.

Cikaken bayannai a kan kasafin kudin na dauke cikin wata takarda da ke majalisar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ciyaman din kwamitin dai-daito, Senata Danjuma Goje ne ya gabatar da sabuwar kasafin kudin.A baya, majalisar ta ce zata amince da kasafin kudin a ranar 24 ga watan Afrilu amma hakan bai yiwu ba.

Wannan ba shi bane lokaci na farko da majalisar ta saka ranar amincewa da kasafin kudin amma aka samu tsaiko.

Kasafin kundin ya kasance yana majalisar dattawar tun 7 ga Nuwambar 2017 lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasfin kudin a zauren majalisar.

Da dumi-dumi: Majalisar tarayya tayi kari kan kasafin kudin 2018

Da dumi-dumi: Majalisar tarayya tayi kari kan kasafin kudin 2018
Source: Twitter

Majalisar kasar da sashin zartarwa sun dade sun ta zargin juna da jan kafa kan amincewa da kasafin kudin na bana

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel