Bayan watanni 6 ana bata lokaci, majalisa zata gabatar da rahoton kasafin kudi a yau

Bayan watanni 6 ana bata lokaci, majalisa zata gabatar da rahoton kasafin kudi a yau

- Watanni shida bayan da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2018, majalisa a yau ta lissafa gabatar da rahoton kasafi cikin al’amurranta na yau

- Rahoton kwamitin majalisar na gabatarwa wanda Sanata Danjuma Goje, ke jagoranta shine na shida a cikin lissafin al’amurran majalisar na yau

- Kasafin da shugaba Buhari ya gabatarwa majalisar tun a 7 ga watan Nuwamba, na shekarar data gabata, wata daya da aka gabatar masa da kasafin a shekarar 2017

Watanni shida bayan da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2018, majalisa a yau ta lissafa gabatar da rahoton kasafi cikin al’amurranta na yau.

Rahoton kwamitin majalisar na gabatarwa wanda Sanata Danjuma Goje, ke jagoranta shine na shida a cikin lissafin al’amurran majalisar na yau.

Kasafin shugaba Buhari ya gabatarwa majalisar tun a 7 ga watan Nuwamba, na shekarar data gabata, wata daya da aka gabatar masa da kasafin a shekarar 2017.

Shawarar shine a mayar da kasafin kudin daga watan Janairu zuwa watan Disamba na kowace shekara.

KU KARANTA KUMA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

Daily Trust ta ruwaito cewa kasafin na baya guda biyu wanda wannan gwamnatin tayi an gabatr dasu ne a watan Disamba, 2016 da 2017, kuma an kaddamar dasu a watan Maris da Afirilu ko wane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel