An sake dage sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta

An sake dage sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta

Wata babban kotun tarayya da ke zama a babban birnin tarayya Abuja ta sake daga cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zarginta da kashe mijinta Bilyaminu Bello dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa Mohammed Bello.

An dage cigaba da sauraron karar ne saboda lauya mai kara wadda ake tuhuma, Mr. Jospeh Daudu bai samu hallartan kotun a yau ba.

Mr Daudu ya aike wa kotu wasika inda ya roki a dage sauraron shari'ar saboda rashin lafiya da ya ke fama da ita.

An sake dage sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta

An sake dage sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta

An tsare wadda ake tuhuma a gidan yari na Suleja da ke Abuja tun ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2017 bisa zarginta da dabawa tsohon mijinta wuka a gidansu da ke Maitama saboda tana zargin yana cin amanar ta yayin data karanta sakon tes a wayarsa.

KU KARANTA: An lalata motocci yayin arangama da 'yan Shi'a su kayi da 'yan sanda a Abuja

Daga baya an garzaya dashi zuwa asibiti amma daga bisani ya ce ga garinku.

Hukumar 'Yansanda na babban birnin tarayya Abuja sun shigar da kara na zarginta da aikata kisan kai amma ta musanta zargin sai dai duk da haka kotu ta bayar da umurnin a tsare ta a gidan yari.

Da farko dai an hana ta beli amma daga baya kotun ta bayar da belinta bayan ta gabatar da rahoton likita da ke nuna cewa bata da lafiya kuma tana dauke da juna biyu saboda haka tana bukatar kulawa na musamman.

Lauya mai kare wadda ake tuhuma ya bukaci kotu tayi fatali da karar da aka shigar saboda babbu wadda hujja da ke nuna cewa Maryam ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi.

Mr Daudu kuma ya kuma ce sammacin da aka aike wa Maryam ya kamata ya fito daga ofishin Alkalin Alkalai na kasa ne ba ofishin 'yan sanda ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel