Masu zanga-zanga don a saki El-Zakzaky sun ce sun shirya Mutuwa

Masu zanga-zanga don a saki El-Zakzaky sun ce sun shirya Mutuwa

- Zanga-zangar da yan shi'a ke gudanarwa na shirin zama rikici

- 'Yan shi'ar sun yi alkawarin ko za'a kashe su sai sun karbo shugabansu

Ƴan ƙungiyar ƴan uwa Musulmai ta ƙasa (IMN) waɗanda aka fi sani da ƴan Shi'a sun sha alwashin bayar da rayuwar su don ganin a saki jagoran nasu Seikh Ibrahim El-Zakzaky da yake tsare tun shekarar 2015.

Masu zanga-zanga don a saki El-Zakzaky sun ce sun shirya Mutuwa

Masu zanga-zanga don a saki El-Zakzaky sun ce sun shirya Mutuwa

Masu zanga -zangar dai sun yiwa babban birnin tarayyan cikar farin ɗango tare da toshe manyan hanyoyin wucewar ababen hawa har na tsawon mintuna 30 kafin daga bisa su yi arangama da jami'an ƴan sanda (NPF) a sakatariyar tarayya.

Wani ganau ya shaidawa majiyarmu cewa, zanga-zangar an fara ta ne cikin lumana kafin daga bisa ta rikiɗe zuwa barazanar da har ta kai ƴan kasuwa da ma'aikata da masu wucewa a ƙafa rugawa domin ceton rayuwarsu.

KU KARANTA: Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan Adam

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin baza su bar Abujan ba har sai an saki shugaban nasu.

"Buhari ka saki shugaban mu." da "Gwamnatin tarayya ta saki El-Zakzaky, bazamu bar Abuja ba har sai an saki shugaban mu."

Wani guda daga cikin masu zanga-zangar mai shuna Muhammed Ali ya bayyanawa majiyarmu cewa, "Mun taru ne a gaban Ma'aikatar yaɗa labarai kusa da mararrabar Majalisar wakilai ka wai sai muka ji ƴan sanda sun kawo mana hari ta hanyar zuba mana ruwan zafi da kuma yin harbi ta ko'ina cikin iskan domin su tarwatsa mu." Shi ne su kuma suka mayar da martani ga ƴan sandan ta hanyar jifa da a cewarsa.

Amina Jibrin wadda ita ma ta fito zanga-zangar ta shaidawa majiyarmu cewa tun daga Kaduna ta taho kuma bata da niyyar komawa har sai an saki Shekh El-Zakzaky.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel