Da yiwuwan ba za’ayi zabe a 2019 ba - Bafarawa

Da yiwuwan ba za’ayi zabe a 2019 ba - Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nuna shakkun yiwuwan zaben Najeriya a shekarar 2019.

Game da cewarsa, Jam’iyyar APC, gwamnatin shugaban Buhari a rikici suke, kuma ba za’a iya yarda da abu mai muhimmanci irin zabe.

Bafarawa a jawabinsa, ya bayyana cewa rashin zaman lafiya da tsaro a kasa, musamman yawan hallakan rayuka da dukiyoyi da wasu makiya Allah keyi babban kalubale ne da za’a fuskanta don yiwuwan zabe a Najeriya nan gaba.

Da yiwuwan ba za’ayi zabe a 2019 ba - Bafarawa

Da yiwuwan ba za’ayi zabe a 2019 ba - Bafarawa
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan ya kara da cewa gwamnati tarayya karkashin APC ta nunawa duniya cewa ba tada hukima, karfi da hazakan gudanar da al’umaran kasa mai rabe-raben kawuna irin Najeriya saboda irin rikice-rikicen da ya faru a zabukan shugabancin da APC ta gudanar kwanakin nan.

KU KARANTA: Ba zamu hana Sanata Omo-Agege shiga majalisa bay au – Majalisar Dattawa

Yace: “Idan APC da gwamnatinta ta gaza shirya zabukan jam’iyya cikin lumana da kwanciyan hankali, ta yaya zata shirya zaben kasa ga baki daya wanda aka kyautata zaton za’a canza mulki?

“Gwamnati ko jami’yyar da bata san me ake cewa demokradiyyan cikin gida ba, ba zata amince da sakamakon zabe ba idan ta sha kasa. Na yi imanin cewa ko an yi zabe , gwamnatin APC ba zata amince ba idan aka lallasa ta; kuma wannan zai shafi zaman lafiya.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel