Dakarun Soji sun ceto wani Dattijo daga hannun 'yan Ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Dakarun Soji sun ceto wani Dattijo daga hannun 'yan Ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Da sanadin wallafa ta shafin jaridar The Punch, hukumar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta bayyana cewar ta sanu nasarar ceto wani Dattijo daga hannun 'yan ta'adda na Boko Haram yayin artabu da gumurzu na musayar wuta a jihar Borno.

Legit.ng ta samu wannan rahoto ne da sanya hannu n kakkin hukumar, Kanal Onyeama Nwachukwu na rukunin dakaru masu yakar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kakakin na rukunin Operation Lafiya Dole ya bayyana cewa, hukumar ta yi nasarar ceto wani dattijo daga hannun 'yan ta'adda na Boko Haram a kauyen Gobara dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Dakarun Soji sun ceto wani Dattijo daga hannun 'yan Ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Dakarun Soji sun ceto wani Dattijo daga hannun 'yan Ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Cikin sanarwar Kanal Onyeama ya kuma bayyana cewa, sakamakon jarumta da sanadin jagorancin Laftanar Asajwun Ahmadu da ya sabo dattijon tsohon a gadon bayan sa yayin wannan ceto.

KARANTA KUMA: Fayemi ya lashe Zaben Fitar da 'Dan Takarar Gwamna na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

A yayin haka kuma, hukumar sojin ta samu nasarar warware wasu bama-bamai a yankunan Damboa da Fadakwe dake garin na Maiduguri.

Hakazalika hukumar ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda tare da kashe biyu daga cikin su gami da samun nasarar cafke wasu muggan makamai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel