Ma’aikacin banki ya alakanta Fayose da wasu kudade N1.2bn da ake tsammanin ya karba daga hannun Dasuki

Ma’aikacin banki ya alakanta Fayose da wasu kudade N1.2bn da ake tsammanin ya karba daga hannun Dasuki

- Shugaban yanki na Zenith Bank Plc, Mista.Lawrence Akande, a ranar Litinin, ya alakanta gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti da wasu kudi N1.2bn wadanda ya karba da Ofishin shugaban tsaro na kasa a shekarar 2014

- Kudaden N1.2bn sune makasudin shari’ar da ake gudanarwa da daya daga cikin jami’an gwamnan, Mista Abiodun Agbele, a gaban Justice Nnamdi Dimgba, a kotun tarayya dake birnin tarayyar

- Hukumar yaki da rashawa a watan Agusta, 2016 ta gurfanar da Agbele tare da wasu mutane uku a gaban kotu bisa laifuka 11 da take zarginsu da aikatawa wanda suka hada da dibar kudaden gwamnati kimanin N4,685,723,000,000

Shugaban yanki na Zenith Bank Plc, Mista Lawrence Akande, a ranar Litinin, ya alakanta gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti da wasu kudi N1.2bn wadanda ya karba da Ofishin shugaban tsaro na kasa a shekarar 2014.

Kudaden N1.2bn sune makasudin shari’ar da ake gudanarwa da daya daga cikin jami’an gwamnan, Mista Abiodun Agbele, a gaban Justice Nnamdi Dimgba, a kotun tarayya dake birnin tarayyar.

Ma’aikacin banki ya alakanta Fayose da wasu kudade N1.2bn da ake tsammanin ya karba daga hannun Dasuki

Ma’aikacin banki ya alakanta Fayose da wasu kudade N1.2bn da ake tsammanin ya karba daga hannun Dasuki

Hukumar yaki da rashawa a watan Agusta, 2016 ta gurfanar da Agbele tare da wasu mutane uku a gaban kotu bisa laifuka 11 da take zarginsu da aikatawa wanda suka hada da dibar kudaden gwamnati kimanin N4,685,723,000,000, wadanda aka karba ta hannun Kanal Sambo Dasuki (rtd) daga asusun ajiya na ONSA dake bankin tarayya na kasa.

KU KARANTA KUMA: Majalisar limamai da malamai na jihar Kaduna sunyi Allah wadai da tsine-tsinen El Rufa'i

Kamfanonin uku da aka gurfanar dasu tare da Agbele sune Sylvan Mcnamara Limited, wanda aka alakanta da tsohon ministan jiha na tsaro, Musiliu Obanikoro; De Privateer Limited wanda Agbele jagoranta, da kuma Spotless Investment Limited, wanda asusun ajiyarsa na banki Fayose da matarsa Feyisetan ke amfani da shi.

Idan dai bazaku manta ba har yanzu tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, Sambo Dasuki na a hannun hukumar DSS yayinda ake cigaba da shari'arsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel